Toshe furofayil, Shafi, ko laƙabin wani a Facebook
Kwafe kafa
Taimakon Manhajar Android
Taimako ta Kwamfuta
Manhajar Taimakon iPad
Taimakon Manhajar iPhone
Taimakon Burauzar Tafi-da-gidanka
Taimako a Manhajar Facebook Lite
Taimakon Manhajar Android
Taimako ta Kwamfuta
Manhajar Taimakon iPad
Taimakon Manhajar iPhone
Taimakon Burauzar Tafi-da-gidanka
Taimako a Manhajar Facebook Lite
Da zarar ka toshe furofayil ko Shafi, za a iyakance wasu ayyuka, kamar yin hulɗa da farfajiyoyin juna, aike, jawabai ko saƙonni. Wannan bai haɗa da manhajoji, wasanni ko ƙungiyoyin da ku duka biyu kuke shiga ciki ba. Idan a halin yanzu kana haɗe da wannan furofayil ko Shafin, toshe shi zai kwance abota, ya cire so kuma ya fasa bin sa.
Da zarar ka toshe laƙabi a cikin ƙungiyar Facebook, ikon wannan laƙabin na yin hulɗa da abubuwan ƙungiyarka zai taƙaita.
Idan kana da ƙarin furofayil ɗin facebook masu yawa , za ka buƙaci kula da toshewa daga kowane ɗaya daga cikin furofayil ɗinka masu yawa a keɓance.
Za ka iya ƙara sani game da yadda za a buɗe furofayil ko Shafi.
Toshe wani furofayil ko Shafi
Don toshe wani mutum a kan Facebook:
- Je ka zuwa Furofayil ko Shafinsu.
- Latsa
Zaɓuka (ko Ƙari).
- Latsa Toshe, sannan ka tabbatar da cewa kana son toshe su ta hanyar latsa Tabbatar.
Haka kuma za ka iya toshe wani ta hanyar zuwa Saituna & Sirri > Saituna > Toshewa da kuma rubuta sunansu.
Lura: Yanzu zaɓin Toshe ba ya samuwa kai tsaye daga mazaɓar wallafa a Ɓangaren Labarai. Har yanzu za ka iya toshe wani mutum daga furofayil ɗinsa ko ta cikin Saitunanka.
Za ka kuma iya toshe furofayil ko Shafi ta hanyar zuwa Saitunan toshewar ka:
- Latsa hoton furofayil ɗinka a sama daga gefen dama na Facebook.
-
Zaɓi
Saituna da tsare-sirri, sai ka latsa
Saituna.
- A cikin mazaɓar, latsa Toshewa a ƙarƙashin Masu sauraro da damar gani.
- A cikin sashin Toshe furofayil da Shafuka, danna Gyara.
- Danna Ƙara a jerin toshewa.
- Shigar da sunan shafi ko furofayil ɗin da kake son toshewa.
- Danna Toshe kusa da sunansu.
- Latsa Tabbatar.
Lura: Idan kana samun matsala wajen neman furofayil ɗin da kake son toshewa, za ka iya gwada amfani da imel mai alaƙa da furofayil ɗin Facebook.
Toshe laƙabi a cikin ƙungiyar Facebook
- Toshe laƙabi a cikin ƙungiyar Facebook.
- Latsa kan laƙabin ko hoton furofayil ɗin laƙabin.
- Kusa da laƙabin a shafin furofayil ɗin ƙungiyarsa, latsa
Zaɓuɓɓuka.
- Latsa Toshe [Laƙabi], sannan ka tabbatar da cewa kana son toshe su ta hanyar latsa Toshe.
- Lura: Toshe laƙabi a cikin ƙungiya yana toshe wannan laƙabin ne kaɗai kuma baya toshe babban furofayil mai alaƙa da wannan laƙabin.
Abin da ke faruwa idan ka toshe furofayil ko Shafi
Idan ka toshe furofayil ko Shafi, wannan furofayil ko Shafin ba zai iya:
- Duba wallafarka.
- A maƙala ka a aike, tsokaci ko hotuna.
- Gayyatar ka zuwa sha’anoni ko rukunai.
- Fara tattaunawa da kai.
- Ƙara ka a matsayin aboki.
Menene ke faruwa idan na toshe laƙabi a cikin ƙungiya?
Idan ka toshe laƙabi a cikin ƙungiya, wannan laƙabin ba zai iya:
- Ya maƙala ka a aike ko jawabai a cikin ƙungiyar.
- Yi hulɗa da abubuwan da ka aike a cikin ƙungiyar.
A wasu lokutan, har yanzu za su iya ganin abubuwan da ka aike. Idan ka toshe laƙabi a cikin ƙungiya, ba za ka ga kowane aike ko jawabai daga laƙabin a cikin wannan ƙungiyar ba. Har yanzu za ka iya ganin abubuwan da laƙabin ya aike a cikin wasu ƙungiyoyin.
Wasu abubuwa da ya kamata a yi la’akari da su a lokacin da aka toshe wani furofayil
- Idan ba ka son yanke abotar furofayil amma kana son ganin kaɗan daga cikin waɗancan wallafa a kan facebook, za ka iya ɗaukar hutu daga wancan furofayil.
- Furofayil ɗin da ka toshe ba zai iya:
- Fara tattaunawa da kai.
- Ƙara ka a matsayin aboki.
- Idan ka toshe furofayil ɗin wani a cikin fiye da ɗaya daga cikin furofayil ɗinka, wannan mutumin da ka toshe zai iya gane cewa kai ne ke mallakar duk waɗancan furofayil ɗin .
Tuna cewar toshe wani mutum ba zai hana dukkan sadarwa ko mu’amala ba (misali: a manhajoji ko ƙungiyoyi) Sami ƙarin bayani game da abin da za ka iya gani a lokacin da ka toshe furofayil ɗin wani.
Idan ka toshe wani wanda ke da fiye da furofayil ɗaya
- Toshewar ɗaya daga cikin furofayil ɗinsu yakan toshe wancan furofayil ne kadai. Ba yakan toshe sauran furofayil ɗin nasu ne ba. Wannan yana nufin za ka iya mu’amala da sauran furofayil ɗinsu.
- Misali, za ka iya fara yin hira tare da sauran waɗancan furofayil ko sanya su a matsayin abokai.
- A lokacin da ka toshe furofayil ɗin wani, hakan zai taƙaice wasu daga hanyoyin da za su iya cuɗanya da kai daga wasu furofayil ɗin su.
Idan ka toshe wani mai laƙabi fiye da ɗaya
Toshe ɗaya daga cikin laƙabansu yana toshe wannan laƙabin ne kaɗai. Ba ya toshe babban furofayil mai alaƙa da laƙabin ko sauran laƙaban da ke da alaƙa da wannan babban furofayil ɗin. Wannan yana nufin cewa har yanzu za ka iya ganin abubuwa daga waɗannan sauran laƙaban ko babban furofayil ɗin da ke da alaƙa da su.
Ka tuna waɗannan abubuwan
- Idan ka toshe wani furofayil sannan ka buɗe shi, akwai buƙatar ka aika wa wannan furofayil da saƙon ƙulla sabuwar abota. Idan ka toshe Shafi sannan ka buɗe shi, za ka buƙaci ka sake bin wannan Shafin.
- Ba za a sanar da Furofayil, Shafuka, da laƙabi ba idan ka toshe su.
Other ways to get help
Chat with Meta AI support assistant
Resolve issues, make changes and get support in real time
